Za’a shafe kwanaki uku ana tafka ruwan sama da guguwa a sassan Nijeriya–Nimet

0
113

Hukumar kula da yanayi ta ƙasa (NiMet) ta sanar da cewa daga Litinin zuwa Laraba za a samu ruwan sama tare da guguwar tsawa a sassa daban-daban na Najeriya.

A cewar sanarwar da ta fitar a Abuja, za a fara da ruwan sama mai sauƙi a wasu yankunan Arewa kamar Taraba da Adamawa da safiya, sannan daga baya a rana a samu guguwar tsawa da ruwan sama a jihohi kamar Kaduna, Gombe, Bauchi, Zamfara, Kebbi da Borno.

Haka kuma a yankin tsakiyar ƙasa, NiMet ta ce za a yi yanayi mai hadari da hasken rana a lokuta, amma akwai yiwuwar ruwan sama da tsawa musamman a Nasarawa, Abuja, Niger da Kogi.

A kudu kuwa, an yi hasashen ruwan sama tsaka-tsaki da guguwar tsawa a jihohin Lagos, Rivers, Akwa Ibom, Cross River, Delta, Ebonyi, Abia da sauran makwabtansu. Hukumar ta kuma yi gargadin yiwuwar ambaliyar ruwa a wasu jihohi musamman Bayelsa, Rivers, Ebonyi da Akwa Ibom.

NiMet ta shawarci jama’a da su yi taka-tsantsan yayin tuki a lokacin ruwan sama, su guji zama kusa da manyan bishiyoyi, su cire na’urorin lantarki daga socket, sannan manoma kada su yi amfani da taki ko magungunan kashe kwari kafin ruwan sama ya sauka don kauce wa asara.

Haka kuma, hukumar ta bukaci hukumomin gaggawa su shirya tunkarar duk wata matsalar ambaliyar ruwa da ka iya tasowa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here