Ousmane Dembélé Ya Lashe Kyautar Ballon d’Or ta 2025
Ɗan wasan gaban Faransa, Ousmane Dembélé, wanda ke bugawa ƙungiyar Paris Saint-Germain da kuma ƙungiyar ƙasar Faransa, ya lashe kyautar Ballon d’Or ta shekarar 2025.
Wannan nasara ta sanya shi cikin manyan ‘yan wasan da suka yi fice a duniya, inda aka yaba masa saboda irin gudummawar da ya bayar ga kulob dinsa da kuma ƙasar Faransa a fannoni daban-daban na wasan ƙwallon ƙafa.
Haka zalika, a bangaren mata, Aitana Bonmatí na ƙungiyar FC Barcelona ta sake lashe kyautar Ballon d’Or ta mata karo na uku a jere, lamarin da ya tabbatar da matsayinta a matsayin jagora a wasan ƙwallon ƙafa na mata.
Kyautar Ballon d’Or dai ita ce babbar lambar yabo a duniyar ƙwallon ƙafa da ake baiwa ‘yan wasa da suka fi fice a kowace shekara.