Muna goyon bayan bashin da Tinubu ke ciyo wa–Kakakin majalisar wakilai

0
55

Kakakin Majalisar Wakilai, Abbas Tajudeen, ya bayyana cewa majalisar tana da cikakken goyon baya ga shirin rancen Shugaba Bola Ahmed Tinubu, yana mai cewa wannan mataki muhimmin ginshiki ne wajen haɓaka tattalin arzikin Najeriya da kuma rage talauci.

Yayin jawabi a taron shekara na 8 na African Network of Parliamentary Budget Offices (AN-PBO) a Abuja, Kakakin ya musanta rahotannin da ke cewa majalisar ta ki amincewa da shirin rancen gwamnatin Tinubu, yana kiran rahotannin da “yaudara”.

Abbas ya ce:

> “Majalisar Wakilai ta 10 da kuma Majalisar Dokoki gaba ɗaya sun jaddada cewa, a halin da ake ciki na gagarumin bukatun ci gaba, rance na da muhimmanci wajen cike gibin kuɗaɗe domin gina muhimman ababen more rayuwa, ƙarfafa tattalin arziki da kuma kare masu rauni. Abin da ya fi muhimmanci shi ne, Shugaban Ƙasa ya tabbatar da cewa dukkan rancen za su kasance masu tsari, gaskiya, da dorewa, tare da bin ƙa’idojin duniya.”

Ya kara da cewa, ƙarƙashin jagorancin Shugaba Tinubu, kuɗaɗen da ake rance za su tafi ne ga muhimman ayyukan da za su ƙara samun kuɗaɗen shiga, kamar wutar lantarki, sufuri, da noma, maimakon kashe su a kan bukatun yau da kullum.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here