Matsalar tsaro ta sa an rufe sansanin masu bautar ƙasa da kasuwanni a Kwara

0
91

Gwamnatin jihar Kwara ta dauki matakin rufe wasu kasuwannin shanu a yankin Kwara ta Kudu da kuma matsar da sansanin masu bautar ƙasa na NYSC daga Yikpata, zuwa Ilorin saboda matsalar tsaro.

Shugabannin ƙananan hukumomi bakwai ne suka bada umarnin rufe kasuwannin don hana ’yan ta’adda samun damar shiga wuraren taruwar jama’a. Sai dai matakin ya haifar da ce-ce-ku-ce daga ’yan kasuwa da ƙungiyar Miyetti Allah, inda suka ce zai lalata harkokin tattalin arziki. Daga baya, an cimma matsaya a taron sarakunan gargajiya cewa a buɗe kasuwannin daga 6 na safe zuwa 6 na yamma kawai.

Haka kuma, hukumar NYSC ta mayar da sansanin Yikpata zuwa Ilorin bayan samun tabbacin tsaro daga gwamnati, abin da mazauna yankin suka yi korafi da cewa zai rage bunƙasar tattalin arziki da suka saba samu lokacin da ’yan bautar ƙasa ke zaune a yankin.

Kwamishinan ’yan sandan jihar ya tabbatar da cewa an samu karin sojoji da motocin sulke don tabbatar da tsaro, yayin da gwamna AbdulRahman AbdulRazaq ya jaddada cewa gwamnati na aiki kafada da kafada da jami’an tsaro da masu ruwa da tsaki domin shawo kan barazanar ta’addanci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here