Sakataren jam’iyyar NNPP, na ƙasa Dr. Ogini Olaposi, ya bayyana cewa shirin shiga APC na Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da magoya bayansa na Kwankwasiya ne kawai, ba na jam’iyyar NNPP ba.
Olaposi ya ce Kwankwaso ya rabu da NNPP tun bayan zaɓen 2023, kuma duk wata tattaunawa da ake yi da shi ta kansa ce, ba ta jam’iyyar ba. Ya ƙara da cewa jam’iyyar yanzu tana maida hankali ne kan gyaran ta a cikin gida da shirye-shiryen zaɓen 2027, bayan rikice-rikicen da suka biyo bayan fitar Kwankwaso da magoya bayansa.
NNPP ta kuma bayyana cewa yarjejeniyar da ta haɗa ta da Kwankwasiya Movement ta ƙare tun bayan kammala zaɓen 2023, tare da zargin tsohon ɗan takararta da ƙoƙarin yi wa jam’iyyar katsalandan kafin ya fice.