Hisbah ta daƙile safarar mata daga Kano zuwa kasashen waje

0
97

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta ce jami’anta sun dakile wani yunkurin safarar mata huɗu daga cikin jihar zuwa kasashen waje.

Hukumar ta bayyana cewa an yaudari matan da alƙawarin samun biza a Ghana, daga nan kuma a tura su zuwa Saudiyya domin neman ayyukan yi.

A cewar hukumar, an ɗauki matakin gaggawa domin kare lafiyar matan tare da nisantar da su daga haɗarin cin zarafi da bautar da su a ƙasashen ketare.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here