Hare haren ƴan ta’adda yayi sanadiyar mutuwar ƴan Najeriya 53 a cikin makonni biyu

0
179

Binciken da jaridar Daily Trust ta tattara daga rahotannin kafofin yaɗa labarai, ya bayyana cewa akalla jami’an tsaro 53 sun rasa rayukansu a fadin Najeriya cikin makonni biyu da suka gabata. Wadanda suka mutu sun haɗa da sojoji, ‘yan sanda, jami’an NSCDC, kwastam, ƴan JTF da kuma kungiyoyin tsaro na al’umma.

Mutane da dama daga cikinsu sun gamu da ajalinsu ne a yayin da suke mayar da martani ga hare-haren ‘yan bindiga, yayin da wasu kuma aka kashe su a wuraren bincike da shingen tsaro.

Hare-hare mafi muni sun faru a jihohin Benue da Kogi, inda aka kashe jami’an tsaro da dama, tare da ƙone motocin sintiri da sace makamai. A Benue, jami’an Operation Zenda da BSCPG sun yi rashin mutane bayan artabu da ‘yan bindiga a Katsina-Ala, inda aka tabbatar da kashe jami’ai, wasu kuma aka sace su. A Kogi kuwa, ‘yan bindiga sun kai farmaki a shingen bincike biyu, inda suka kashe jami’an ‘yan sanda hudu da wani farar hula.

A wani ɓangare kuma, rundunar ‘yan sanda ta sanar da cafke mutum shida da ake zargi da hannu a harin Benue, yayin da aka gurfanar da wasu a gaban kotu bisa zargin kisan kai da safarar makamai.

Baya ga kashe jami’an tsaro, rahotanni sun nuna cewa ‘yan bindiga sun ƙara kai hare-hare a wasu jihohi kamar Zamfara, Katsina, Niger, Edo, Borno, Kebbi, Abuja da Kwara, inda aka kashe jami’an tsaro da fararen hula da dama tare da yin garkuwa da wasu.

Gwamnoni da hukumomin tsaro sun yi Allah wadai da hare-haren, suna mai kiran al’umma da su ci gaba da haɗa kai domin dakile wannan barazana ga zaman lafiya da tsaron ƙasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here