Ganduje Ya Jagoranci Saukar Alqur’ani, Da Musuluntar Da Maguzawa a Kano

0
39

Tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma tsohon Shugaban Jam’iyyar APC na kasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, CON, ya jagoranci taron saukar Alqur’ani mai girma tare da musuluntar da akalla mutane 280 daga cikin maguzawa a gidansa da ke Kano.

Dr. Ganduje, ya bayyana cewa addu’o’in da ake gudanarwa a wurare daban daban irin wanda yake ɗaukar nauyi na nufin neman alkhairi ga Jihar Kano da Najeriya baki daya.

A yayin taron, Ganduje tare da iyalansa sun yi jawabi ga waɗanda aka musuluntar tare da mika musu kyaututtuka. Ya jaddada cewa babban burinsa shi ne ganin ‘ya’yansa sun gaje shi wajen ci gaba da gudanar da ayyukan alkhairi da gidauniyar Ganduje ke jagoranta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here