Hukumar kula da fursunoni ta Najeriya, reshen Kano, ta sanar da cewa fursunoni 68 sun ci jarabawar kammala sakandire ta NECO 2025.
A cikin sanarwar da hukumar ta fitar, an bayyana cewa wannan nasara ta kasance abin farin ciki ga fursunonin, inda suka ce tana ba su sabon fata na sauya rayuwarsu gaba ɗaya.
Hukumar ta bayyana cewa nasarar ta samu ne saboda tallafin gwamnatin Kano, wadda ta ɗauki nauyin ci gaban ilimin fursunonin.
> “Wannan shiri ya yi daidai da dokar hukumar kula da fursunoni ta Najeriya ta 2019, wadda ta fi mayar da hankali kan gyara da sake tarbiyyar fursunoni ta hanyar ilimi da kuma horar da su a sana’o’i,” in ji sanarwar.
Gwamnatin Kano ta kuma jaddada cewa tana da niyyar ci gaba da samar da damarmakin ilimi ga fursunoni, domin taimaka musu su zama nagari a cikin al’umma.