An yi sulhu tsakanin Mai Dubun Isa, da  Mai Tajil’izzi

0
65

A yau Litinin, 22 ga watan Satumba, 2025, Shugaban Majalisar Malamai ta Jihar Kano, Malam Ibrahim Khalil, ya gudanar da taron sulhu tsakanin fitattun sha’iran jihar, Malam Usman Mai Dubun Isa da Shehi Ahmad Mai Tajil’izzi.

Taron ya gudana ne domin sasanta sabanin fahimtar da ya kunno kai tsakaninsu kan batun kirari da yabo ga fiyayyen halitta, Annabi Muhammad (SAW).

Shugaban Majalisar Malaman ya bukaci ɓangarorin biyu da su rungumi hakuri da jituwa, tare da ci gaba da amfani da baiwar da Allah ya ba su wajen yada kauna da hadin kai a cikin al’umma.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here