Shugaban Hukumar Yaki da Sha da Miyagun Kwayoyi (NDLEA), Janar Buba Marwa (rtd), ya bayyana cewa shaye-shaye na daga cikin manyan dalilan da ke haddasa rashin tsaro a Najeriya.
Ya bayyana haka ne a Abuja yayin bikin cika shekaru 38 da kammala makarantar soja ta NMS Zaria, inda ya ce miyagun kwayoyi na haifar da ta’addanci, rikice-rikice da kuma lalata tarbiyya a cikin al’umma.
Marwa ya bayyana cewa cikin shekaru biyu da suka gabata NDLEA ta cafke fiye da magungunan Tramadol miliyan 1.8, robon Codeine miliyan 400, da kuma kwayar Captagon 500,000 da aka boye a cikin injuna da ake zaton za a kai wa ‘yan ta’adda.
Ya jaddada bukatar iyaye, makarantu, kungiyoyin addini da kafafen yada labarai su hada kai wajen dakile matsalar shaye-shaye, yana mai cewa: “Duk inda aka samu miyagun kwayoyi, to za a samu rashin tsaro da ta’addanci.”
A nasa jawabin, Shugaban Hafsan Sojojin Kasa (CDS), Janar Christopher Musa, wanda aka wakilta, ya tabbatar da cewa rundunar soji za ta ci gaba da kare martabar kasa tare da tabbatar da doka da oda.