Gwamnati ta fara binciken baƙuwar cutar dake cin naman mutane a Adamawa

0
119

Gwamnatin Tarayya ta fara bincike a kan wata sabuwar cuta mai cinye naman jikin ɗan adam da ta kashe mutane 7 a Malabu, Adamawa. 

Rahoto ya nuna cewa an tabbatar da mutane 67 sun kamu da ita, inda takwas ke jinyat tiyatar da aka yi musu a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Modibbo Adama (MAUTH), Yola.

Shugaban shirin kula da tarin fuka da Buruli Ulcer, Dr. Adesigbin Olufemi, ya ce cutar tana farawa ne da ƙuraje kafin ta fashe, sannan ta fara cinye nama har ma ta iya lalata ƙashi.

Ya ce ana zargin Buruli Ulcer, ce cutar da ta kama mutanen da ƙwayar Mycobacterium ulcerans ke haifarwa, wacce ake samu a wuraren ruwan da baya tafiya.

Ya gargadi jama’a da su rika neman magani da wuri, ba wai su danganta cutar da sihiri ba, tare da jaddada cewa tsafta da ingantaccen ruwan sha na da muhimmanci wajen dakile yaduwar cutar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here