Burtaniya ta amince da Falasɗinu a matsayin ƙasa mai iko

0
88

Fira Ministan Birtaniya, Sir Keir Starmer, ya sanar a ranar Lahadi cewa ƙasarsa ta amince da Falasɗinu a matsayin ƙasa mai cikakken iko.

Starmer ya bayyana hakan ne a shafinsa na X, inda ya ce: “A yau, domin farfaɗo da fatan samun zaman lafiya tsakanin Falasɗinu da Isra’ila ta hanyar mafita ta ƙasashe biyu, Birtaniya ta amince da Falasɗinu a matsayin ƙasa.”

Tun a watan Yuli, Fira Ministan ya nemi gwamnatin Benjamin Netanyahu ta daina amfani da yunwa a Gaza a matsayin makami tare da buɗe hanyar agaji. Ya kuma gargadi cewa rashin yin hakan zai sa Birtaniya ta amince da Falasɗinu.

Birtaniya ta dauki wannan mataki ne a daidai lokacin da ake shirin buɗe zaman Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 80 a New York. Haka zalika, Kanada da Ostiraliya sun sanar da amincewarsu ga Falasɗinu a ranar Lahadi, bayan kasashe irin su Ireland, Spain da Norway da suka riga su tun bara.

Masani kan harkokin Gabas ta Tsakiya, Dr Julie Norman daga UCL, ya ce wannan mataki ba lallai ya kawo sauyi kai tsaye ba, amma yana da muhimmanci a matsayin matsayar diflomasiyya da goyon baya ga Falasɗinu, musamman a lokacin da rikici ya tsananta a Gaza da Yammacin Kogin Jordan.

Ta kara da cewa wannan na iya kawo sauyi a London, misali bude ofishin jakadancin Falasɗinu a Birtaniya, fiye da yadda zai yi tasiri kai tsaye a Ramallah.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here