Babu wanda zai ce na taɓa neman wa’adin mulki na uku–Obasanjo

0
89

Babu wanda zai ce na taɓa neman wa’adin mulki na uku–Obasanjo

Tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo, ya musanta zargin da aka dade ana yi cewa ya nemi tsawaita wa’adin mulkinsa lokacin yana kan karaga.

Da yake jawabi a taron tattaunawa kan makomar dimokuraɗiyya na cibiyar Goodluck Jonathan a Accra, Ghana, Obasanjo ya ce babu wani ɗan Najeriya mai rai ko mamaci da zai iya cewa ya taɓa roƙon goyon baya don neman wa’adin mulki na uku.

“Ina sane da yadda ake samun abubuwa a siyasa. Idan da ina so, zan san yadda zan yi. Amma babu wanda zai ce na taɓa kiran shi na ce ina neman wa’adin mulki na uku,” in ji shi.

Ya kara da cewa samun sassaucin bashi na ƙasa da ya yi wa Najeriya a mulkinsa ya fi wahalar cimma fiye da batun wa’adin mulki na uku.

Obasanjo ya yi gargadi ga shugabanni masu son dawwama a kan mulki, yana mai cewa irin wannan tunani na rashin maye gurbin kowa babban “laifi a wajen Allah.”

Shi ma tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan, wanda ya halarci taron, ya ce matsalar manyan shugabanni a Afirka ita ce magudi a zaɓe. A cewarsa, idan an gudanar da sahihin zaɓe, shugaba marar nagarta zai fuskanci ficewa ta hanyar ƙuri’ar al’umma.

Jonathan ya yi kira ga shugabannin Afirka su sake tunanin tsarin dimokuraɗiyya domin kare muradun jama’a, inda ya jaddada bukatar su bai wa al’umma damar jin daɗin ‘yanci, tsaro, ilimi, lafiya, aikin yi da mutunci.

Taron ya samu halartar shugaban hukumar ECOWAS, Dr. Omar Touray, da Bishop Matthew Hassan Kukah, inda aka jaddada cewa dimokuraɗiyya a Afirka dole ta wuce zaɓe kaɗai, ta haɗa da gaskiya, hidima da ɗa’a.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here