Gwamnati ta dage kan kammala aikin titin Abuja–Kaduna–Kano a 2026
Ministan Ayyuka, David Umahi, ya jaddada cewa gwamnati za ta tsaya tsayin daka wajen ganin an kammala aikin titin Abuja–Kaduna–Kano mai tsawon kilomita 700 nan da watan Yuni na shekarar 2026.
Umahi ya bayyana haka ne a lokacin da ya kai ziyarar duba aikin da ake yi a kan hanyoyin Abuja–Kaduna a ranar Asabar.
Ya ce daga yanzu gwamnati za ta daina biyan kwangila bisa takardar shaida kawai, sai dai ta dora mahimmanci kan kammala matakai na musamman kafin a biya. Ministan ya yi nuni da cewa wannan aiki babban ginshikin ci gaban yankin Arewa ne.