Fargaba da alhini sun sake mamaye al’ummar jihar Sokoto bayan hatsarin jirgin ruwa da ya yi ajalin mutane da dama a ƙaramar hukumar Sabon Birni.
Lamarin ya faru ne lokacin da mazauna garuruwan suka yi yunkurin tserewa daga wani sabon hari da ‘yan ta’addan Lakurawa suka kai musu. Shaidun gani da ido sun bayyana cewa mutane da yawa sun shiga jirgin ruwa mai ɗauke da kaya da jama’a fiye da ƙima, lamarin da ya sa ya kife a tsakiyar ruwa.
Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Sokoto ta tabbatar da aukuwar hatsarin, inda ta ce ana ci gaba da aikin ceto domin gano gawarwakin da aka rasa. Sai dai ba a tabbatar da adadin mutanen da ke cikin jirgin ba a lokacin hatsarin.
Wannan na zuwa ne a matsayin hatsarin jirgin ruwa na huɗu cikin watanni biyu kacal a jihar, abin da ke ƙara tayar da hankula kan haɗarin tsaro da rashin tsari wajen amfani da hanyoyin ruwa.