Harin Boko Haram ya tilastawa dubban mutane tserewa daga Borno zuwa Kamaru
A kalla fararen hula 5,000 ne suka tsere zuwa ƙasar Kamaru bayan da ‘yan ta’adda suka kai mummunan hari a wasu garuruwa biyu na Jihar Borno da ke arewa maso gabashin Nijeriya.
Harin ya auku ne a daren Juma’a a garuruwan Banki da Freetown, waɗanda ke kusa da iyakar Nijeriya da Kamaru. Shaidu da majiyoyin tsaro sun tabbatar da cewa maharan sun yi ƙoƙarin kwace sansanin soja na Banki, lamarin da ya jawo tserewar jama’a da dama.
Wata mazauniyar Banki mai suna Amina Bakari ta ce: “Ko’ina mutane suna ihu suna gudu, saboda tsoron kada a kashe su. Ni ma na tsere na haye iyaka zuwa Kamaru.”
Rahotanni sun nuna cewa mayaƙan Boko Haram ne suka kai harin, sai dai jami’an tsaro sun ce an samu goyon bayan dakarun sama da ya taimaka wajen fatattakar su. Duk da haka, sojoji biyu da fararen hula biyu sun rasa rayukansu, tare da lalata gidaje da dama.
Ayuba Isa, mataimakin kwamandan sansanin Banki, ya ce sojojin sun nuna bajinta wajen kare sansanin daga hannun maharan. “Mutanenmu sun yi iyakar ƙoƙari, har muka kori maharan. Amma abin takaici, fararen hula da yawa sun tsere kuma gidaje sun lalace,” in ji shi.
Tun daga shekarar 2009, rikicin Boko Haram da ISWAP ya yi sanadin mutuwar sama da mutane 40,000, ya kuma tilasta wa miliyoyin ‘yan Nijeriya barin muhallansu, a cewar Majalisar Ɗinkin Duniya.