Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Najeriya (EFCC) ta bayyana cewa ta kama mutum 37 da ake zargi da aikata zamba ta yanar gizo a Warri, Jihar Delta, da kuma Owerri, Jihar Imo.
Wannan samame ya samu ne a ranar Juma’a, 19 ga Satumba, 2025, bisa sahihan bayanai da hukumar ta samu kan ayyukan su na damfara da cinikayyar kudaden intanet.
Rahotanni sun nuna cewa an kama su ne yayin da suke amfani da na’urorin zamani wajen damfarar mutane. Babban wanda ake zargi da jagorantar su, Robert Ebuka Chukwuedo, ya tsere daga gidansa da ke Warri lokacin da jami’an EFCC suka kai samame. Sai dai an kama wasu daga cikin abokan harkallarsa a cikin gidan.
Kayan da aka gano daga wajen su sun haɗa da motocin alfarma, wayoyi, kwamfutoci da kuma kayan tsafi.
EFCC ta ce za a gurfanar da su a kotu bayan kammala bincike.