Ambaliya ta kashe mutane uku da lalata gidaje fiya da dubu a Adamawa

0
55

Ambaliya ta kashe mutane uku da lalata gidaje fiya da dubu a Adamawa

Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) ta tabbatar da cewa mutum uku sun rasu, yayin da gidaje fiye da 1,415 suka shiga cikin halin tsaka mai wuya sakamakon ambaliyar ruwa a Jihar Adamawa.

Ambaliyar, wadda ta afku bayan ruwan sama mai tsanani a ranar Talata, ta shafi al’ummomi da dama a ƙananan hukumomin Yola ta Arewa da Yola ta Kudu.

Rahoton NEMA tare da Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Adamawa (ADSEMA) da wasu hukumomi suka fitar ya nuna cewa ƙauyuka 13 ne abin ya shafa. Sama da mutane 40 sun jikkata, yayin da gonaki da muhimman kayayyakin more rayuwa suka nutse cikin ruwa.

Wasu daga cikin iyalan da suka rasa matsuguni na samun mafaka a wuraren karɓar baki, yayin da wasu aka mayar da su sansanin ƙaura na ambaliya da ke Girei.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here