Babu ayyuka huɗu da Ganduje ya kammala a zamanin mulkin sa–Abba
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya soki tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje, bisa rashin gudanar da muhimman ayyukan raya kasa a tsawon shekaru takwas da ya yi a mulki tare da cinye dukiyar jihar.
Yusuf ya yi wannan furuci ne a ranar Alhamis yayin raba takardun ɗaukar aiki na ɗin-din-ɗin ga malamai 4,315 a karkashin shirin Better Education Service Delivery for All (BESDA). Ya kalubalanci Ganduje da ya fito ya nuna aƙalla ayyuka hudu da ya kammala a wa’adin mulkinsa.
A cewarsa, gwamnatin da ta gabata ta zalunci malamai, ma’aikata da ’yan fansho, inda ake sayar da guraben aiki, tare da barin asusun jihar a matsayin mara kudi har ma ya kai matsayi na N9,075 a lokacin da aka mika mulki.
Sai dai ya bayyana cewa gwamnatin sa ta toshe ɓarakar almundahana, inda aka adana biliyoyin naira da ake karkatarwa, yanzu kuma ana mayar da su kan ayyukan ci gaba.
Yusuf ya ce:
> “Idan har suna da gaskiya, su fito su nuna mana aƙalla ayyuka hudu da suka kammala a cikin shekaru takwas.”
Daga cikin abubuwan da gwamnatinsa ta fara, gwamnan ya ambaci daukar malamai, gina da gyara makarantu, shirye-shiryen tallafawa manoma, biyan fansho, sake buɗe makarantun kwana, hasken tituna da shirye-shiryen ƙarfafa tattalin arziki.
Haka kuma, gwamnan ya umarci hukumar SUBEB da ta ɗauki karin malamai a karkashin BESDA, tare da sanar da bayar da lamunin N100,000 ga malamai 2,000 domin tallafa musu.