An samu gawar kwamandan hukumar NDLEA a ɗakin Otal

0
8

Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi (NDLEA) ta shiga cikin jimami bayan an samu rahoton mutuwar kwamandanta a jihar Cross River, Morrison Ogbonna, a wani otal da ke Calabar.

Rahotanni sun bayyana cewa abokan aikinsa sun je daukarsa domin wani aiki da safiyar Alhamis, amma suka tarar ya kasa buɗe kofar ɗakin da yake ciki. 

Daga bisani, bayan da aka buɗe ɗakin tare da shugabannin otal ɗin, an tarar da gawarsa.

Ogbonna, wanda aka tura jihar a watan Agusta domin ya maye gurbin Rachel Umebuali, ya rasu ba tare da wata alamar rashin lafiya ta bayyana ba, lamarin da ya tayar da hankula.

Kakakin rundunar ‘yan sanda ta Cross River, Irene Ugbo-Obase, ta tabbatar da faruwar al’amarin, inda ta ce bincike yana gudana don gano ainihin musabbabin mutuwarsa.

A halin yanzu, hukumar NDLEA ba ta fitar da wata sanarwa kan wannan lamari ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here