Majalisar dokokin Rivers zata binciki gwamnan riƙon jihar kan kuɗaɗen da ya kashe
Majalisar Dokokin Jihar Rivers ta amince da fara bincike kan yadda aka tafiyar da kudaden jihar a lokacin mulkin Ibok-Ete Ibas, wanda ya yi wa’adin wata shida a matsayin mai kula da jihar bayan da aka kafa dokar ta-baci.
Majalisar ta koma zaman aiki a ranar Alhamis bayan Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya kawo ƙarshen dokar ta-bacin da ya kafa a jihar tare da dawo da tsarin dimokuraɗiyya.
A zaman da kakakin majalisar, Martins Amaewhule, ya jagoranta, an umurci Gwamna Siminalayi Fubara da ya gabatar da kasafin kuɗin shekarar 2025 don tattaunawar majalisar. Haka kuma, majalisar ta buƙaci gwamnan ya aiko da jerin sunayen waɗanda zai naɗa a matsayin kwamishinoni domin tantancewa da tabbatarwa.
Zaman majalisar ya gudana a dakin taro na sansanin ‘yan majalisar, kasancewar ginin majalisar da ke Port Harcourt har yanzu yana cikin gyara bayan rusa shi a farkon shekarar nan.
Tun a ranar 18 ga Maris 2025 ne Shugaba Tinubu ya kafa dokar ta-baci a jihar saboda rikicin siyasa tsakanin Gwamna Fubara da Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, wanda ya sa aka dakatar da Fubara, mataimakiyarsa Ngozi Nma Odu da kuma ‘yan majalisar, sannan aka naɗa Ibas a matsayin mai kula da jihar na wucin gadi.