Kaduna ta fara aiwatar da mafi ƙarancin albashi na Naira 72,000 ga ma’aikata

0
27

Gwamnatin jihar Kaduna ta fara aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashi na ₦72,000 ga ma’aikatan matakai na 1 zuwa 6, kamar yadda reshen kungiyar kwadago ta NLC a jihar ya tabbatar.

Shugaban NLC na jihar, Ayuba Magaji Suleiman, ya bayyana matakin a matsayin ci gaba mai kyau, amma ya nuna damuwa cewa akwai ma’aikata da dama da ba su amfana ba, musamman malaman makarantu, ma’aikatan kananan hukumomi da na asibitocin kula da lafiya a matakin farko.

Ya ce aiwatar da cikakken tsarin zai biyo bayan kammala aikin tantance ma’aikata da masu ritaya da ake gudanarwa, wanda ake sa ran kammalawa kafin karshen watan Satumba 2025.

Suleiman ya kuma yaba da shirin gwamnati na sabunta jadawalin albashi ga ma’aikatan lafiya karkashin tsarin CONMESS da CONHESS, domin daidaita su da sabon mafi ƙarancin albashi.

Kungiyar kwadagon ta sha alwashin ci gaba da sa ido tare da matsa lamba kan gwamnati domin tabbatar da cewa dukkan ma’aikata, ciki har da malaman manyan makarantu, ma’aikatan lafiya da na kananan hukumomi, sun amfana da sabon albashi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here