Kwamitin Rabon Kuɗaɗen Tarayya (FAAC) ya bayyana cewa an raba jimillar kuɗi Naira triliyan 2.225 a watan Agusta 2025 ga Gwamnatin Tarayya, Jihohi da Kananan Hukumomi. Wannan adadi ya karu da Naira biliyan 224.1 (11.2%) idan aka kwatanta da Naira triliyan 2.001 da aka raba a watan Yuli.
A cewar sanarwar da ofishin Akanta Janar na Ƙasa ya fitar, kuɗaɗen sun haɗa da Naira triliyan 1.478 daga kudaden haraji, Naira biliyan 672 daga VAT, Naira biliyan 32.3 daga kudin e-Transfer, da kuma Naira biliyan 41.2 daga bambancin musayar kuɗi.
Daga cikin rabon, Gwamnatin Tarayya ta samu N684.4bn, Jihohi N347.1bn, Kananan Hukumomi N267.6bn, yayin da jihohin masu samar da mai suka karɓi N179.3bn a matsayin kaso na 13% na albarkatun mai.
Wannan karin kudin ya nuna shi ne karo na uku a jere da kudaden shiga suka ci gaba da karuwa.