Fubara ya karɓi ragamar gwamnatin jihar Rivers
Gwamnan Jihar Rivers, Siminalayi Fubara, ya koma ofis bayan dage dokar ta baci da Shugaba Bola Tinubu ya sanya a jihar. Rear Admiral Ibok-Ete Ibas, wanda ya yi aiki a matsayin gwamnan rikon kwarya tsawon watanni shida, ya mika mulki gare shi a hukumance ranar Talata.
A jawabin bankwana da ya gabatar, Ibas ya gode wa al’ummar jihar bisa goyon bayan da suka bashi, inda ya ce an samu nasarorin da suka hada da gudanar da zaben kananan hukumomi, kafa sabbin hukumomi da kwamitoci, da kuma tabbatar da bin doka da oda.
Ya kuma ja hankalin jama’ar Rivers da su marawa Gwamna Fubara baya domin ci gaban jihar, yana mai jaddada cewa jagoranci ba zai yi tasiri ba idan babu goyon bayan al’umma.
Shugaba Tinubu ne ya dakatar da Fubara a baya tare da mataimakiyarsa da mambobin majalisar dokoki, saboda rikicin siyasa da ya dabaibaye jihar.