NECO ta saki sakamakon jarabawar SSCE na 2025
Hukumar shirya jarrabawar kammala makarantun sakandire ta ƙasa (NECO) ta sanar da sakin sakamakon jarabawar (SSCE) na shekarar 2025.
A cewar maga takardan hukumar, Farfesa Dantani Ibrahim Wushishi, cikin ɗaliban da suka rubuta jarabawar, kashi 60.26% sun samu Credits biyar da suka haɗa da Turanci da Lissafi, wanda shi ne mafi ƙarancin sharadin shiga jami’a a Najeriya.
Haka kuma, ya bayyana cewa ɗalibai 1,144,496 (84.26%) sun samu Credits biyar ko fiye ba tare da la’akari da Lissafi da Turanci ba.
Jimillar ɗalibai 1,367,210 ne suka yi rajista da suka haɗa da maza 685,514 da mata 681,696, yayin da 1,358,339 suka zauna jarabawar.
Wannan sanarwa ta fito ne daga babban ofishin hukumar da ke Minna, Jihar Neja a yau Laraba.