Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ƙasa EFCC ta ce yawaitar zamba ta yanar gizo na haddasa wa ’yan Najeriya masu bin doka matsalolin samun visa zuwa ƙasashen waje.
Shugaban hukumar, Ola Olukoyede, ya bayyana cewa laifukan ‘yahoo-yahoo, halatta kudaden haram da satar arziƙin ƙasa suna jawo wa Najeriya asarar biliyoyin naira da kuma bata sunan ƙasa a idon duniya.
Ya gargadi matasa da su guji zamba, su mayar da hankalinsu kan sana’o’in kirkire-kirkire kamar fasaha, kasuwanci da noma, yana mai cewa: “Zamba tarko ce, ba nasara ba.”
Olukoyede ya tabbatar da cewa EFCC za ta ƙara kaimi wajen wayar da kai da kuma yaki da laifukan yanar gizo.