Gwamnatin Tarayya ta bayyana sabbin shirye-shirye na zuba jari a fannin noma da ake sa ran za su iya samar da ayyukan yi miliyan 21 a fadin ƙasar nan.
Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ne ya bayyana haka a wani taro da aka gudanar a Abuja, inda ya ce gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta shirya matakan da za su haɗa da faɗaɗa noman zamani, samar da ruwa domin ban ruwa, sauƙaƙe hanyoyin samun lamunin kuɗi ga manoma, da kuma kafa tsarin rajistar filaye cikin sauƙi.
> Shettima ya bayyana cewa yunwa ita ce babbar jarabawa da ke bayyana raunin jama’a da ƙalubalen da suke fuskanta a rayuwa.
A cewar sanarwar da kakakin ofishinsa ya fitar, gwamnati na shirin saka hannun jari a manyan injinan noma da kuma ayyukan ban ruwa domin ƙarfafa samar da abinci a gida.
Dalilin sauya salo
Rahoton ya nuna cewa hauhawar farashin kayan abinci da sauyin yanayi sun ƙara bayyana muhimmancin zuba jari a harkar noma.
Najeriya ta dade tana dogaro da shigo da abinci daga ƙasashen waje, abin da ya ƙara tsananta bayan cire tallafin mai da kuma sauya tsarin kuɗi a shekarar 2023, wanda ya haddasa tsananin hauhawar farashi.


