Dangote: Kamfanin ƙarafa na Ajaokuta ba zai taɓa dawo wa aiki ba

0
167

Dangote: Kamfanin ƙarafa na Ajaokuta ba zai taɓa dawo wa aiki ba

Shahararren attajirin Afrika, Aliko Dangote, ya bayyana cewa ba ya ganin kamfanin karafa na Ajaokuta Steel Company, zai farfaɗo ko yin aiki yadda ake bukata.

A cikin wani faifan bidiyo da aka wallafa a shafin TVC a X ranar Talata, Dangote ya jaddada muhimmancin masana’antar ƙarafa wajen bunƙasa masana’antu da tattalin arzikin ƙasa. Amma ya ce matsalolin da suka daɗe suna damun Ajaokuta sun riga sun wuce gyara.

Dangote ya kwatanta ƙoƙarin dawo da Ajaokuta da yunƙurin amfani da tsohuwar fasaha a duniyar da sabbin na’urori suka mamaye, yana mai cewa lokaci da ci gaban zamani sun riga sun wuce wannan shiri.

> “Babu wata ƙasa da za ta bunƙasa ba tare da masana’antar ƙarafa ba. Amma gaskiya shi ne, Ajaokuta ba zata gyaru ba. Muna iya ci gaba da ruɗar kanmu amma abin ba zai yiwu ba,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa komawa kan Ajaokuta kamar tayar da matattu ne daga kabari, wanda ya ce “abu ne da ba zai yiwu ba kwata-kwata.”

Tarihin Ajaokuta Steel

Kamfanin karafan na Ajaokuta da ke Jihar Kogi an fara gina shi tun daga shekarar 1979 zuwa tsakiyar shekarun 1990, amma bai taɓa kammaluwa ko yin aiki yadda ya kamata ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here