Buhari ne ya lalata tattalin arzikin Najeriya ba Tinubu ba–Dogara

0
18

Tsohon shugaban Majalisar Wakilai, Yakubu Dogara, ya zargi gwamnatin marigayi Muhammadu Buhari da lalata tattalin arzikin Najeriya ta hanyar buga kuɗi da ɗaukar rancen kasashen waje ba tare da tsari ba.

Dogara ya bayyana cewa sama da Naira tiriliyan 22.7 aka buga a lokacin Buhari, abin da ya jefa ƙasar cikin mawuyacin hali. Ya ce tsarin musayar kuɗi na wancan lokaci ya bai wa wasu damar samun riba ba tare da samar da kaya ba.

Ya kuma jaddada cewa lokacin da Shugaba Bola Tinubu ya hau mulki, tattalin arzikin ƙasar ya riga ya zama “gurbatacce,” amma matakan gyara da gwamnatin Tinubu ta fara suna da muhimmanci wajen dawo da daidaito.

Dogara ya yaba da kafa kwamitin haraji ƙarƙashin jagorancin Dr. Taiwo Oyedele, yana mai cewa shawarwarin sauye-sauyen su na iya kawo adalci da daidaito a tsarin tattalin arzikin ƙasa.

Sai dai ya yi gargadin cewa sauye-sauyen tattalin arziki na fuskantar adawa daga masu cin gajiyar tsohon tsarin, don haka nasara tana buƙatar jajircewa da haɗin kai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here