APC Na Neman Fubara Ya Sauya Sheka Zuwa Cikin Ta

0
19

Yayin da wa’adin dokar ta-baci a Jihar Rivers ke karewa gobe, jam’iyyar APC ta kira Gwamna Siminalayi Fubara da ya bar PDP ya koma cikinsu.

Tun a watan Maris 2025, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da Fubara, mataimakiyarsa da ‘yan majalisar jiha tare da nada tsohon hafsan soji, Vice Admiral Ibok-Étè Ibas (rtd), a matsayin mai rikon kwarya. Wannan mataki an ɗauke shi ne saboda rikicin siyasa tsakanin Fubara da tsohon gwamnan jihar, Nyesom Wike, wanda yanzu ke rike da kujerar Ministan FCT.

Da yake magana, Daraktan Yaɗa Labarai na APC na ƙasa, Bala Ibrahim, ya ce shigar Fubara cikin APC zai ƙara wa jam’iyyar ƙima tare da taimaka musu wajen cimma burinsu na lashe dukkan jihohin Najeriya nan gaba. Haka kuma, shugaban APC na jihar Rivers, Darlington Nwauju, ya ce idan shi ne Fubara, zai yi amfani da damar dawowa mulki ya sanar da sauya sheka cikin gaggawa.

Sai dai PDP ta gargadi Fubara da kada ya amince da kiran APC. Mataimakin mai magana da yawun PDP na ƙasa, Mallam Ibrahim Abdullahi, ya bayyana cewa shiga APC tamkar “kabarin siyasa ne ga Fubara.” Haka nan wani mamba na NEC na PDP, Timothy Osadolor, ya ce APC na ƙoƙarin cin gajiyar abin da ba ta shuka ba.

Ana sa ran Fubara zai koma mulki ranar Alhamis bayan karewar dokar ta-baci, lamarin da zai iya ƙara zafafa rikicin siyasar jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here