Yan bindiga sun kai hari masallaci tare da sace masallata a Zamfara 

0
18

Rahotanni daga jihar Zamfara sun tabbatar da cewa ‘yan bindiga sun kai farmaki wani masallaci da ke ƙauyen Gidan Turbe a ƙaramar hukumar Tsafe, inda suka sace akalla mutane 40 da ke cikin sallah a asubahin Lahadi.

Shaidu daga yankin sun ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 5:30 na safe, lokacin da mazauna ƙauyen ke tsaka da ibada, sai gungun ‘yan bindiga suka kewaye masallacin tare da tilasta wa masu ibada bin su cikin dazukan da ke kusa da Gohori.

Harin ya biyo bayan wani makamancin sa da aka kai a ƙauyen Godai na ƙaramar hukumar Bukkuyum, inda aka kuma sace mutane fiye da 10.

Wannan lamari na nuna rushewar yarjejeniyar sulhu da wasu shugabannin al’umma da jami’an tsaro suka kulla da ‘yan bindiga a wasu yankuna na arewa maso yamma, musamman a Katsina da Zamfara.

Duk da cewa dakarun sojoji da jami’an tsaro na ci gaba da gudanar da sama da kasa a jihohin Katsina, Kebbi da Zamfara, inda ake kai wa ‘yan ta’adda farmaki da kuma kwato makamai da babura, sai dai har yanzu hare-haren na cigaba da ƙaruwa a sassa daban-daban.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here