Dakarun Operation Hadin Kai (OPHK) sun kashe ‘yan ta’addan ISWAP guda takwas a wani samame da suka yi a kusa da Garin Giwa, a hanyar Baga–Cross Kauwa, jihar Borno.
Rahotonni sun bayyana cewa mayakan sun yi ƙoƙarin dakile aikin sojojin, amma hakan bai yiwu ba, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar shugabanninsu biyu (Munzirs) da Qaid.
Daga cikin waɗanda aka kashe akwai Modu Dogo Munzir na Dogon Chukun da Abu Aisha Qaid na Tumbun Mota. Wasu daga cikin su kuma sun tsere da raunuka, inda suka bar babura 14 da aka kwace.
Rundunar sojin ta tabbatar da cewa za ta ci gaba da kawar da ayyukan ta’addanci a yankin Arewa maso Gabas domin dawo da zaman lafiya.
A baya-bayan nan, an kashe mayakan ISWAP sama da 35 a wani samame da aka kai a yankin Kumshe, kusa da iyakar Borno.