Hukumar Tace Fina-Finai da Dab’i ta Jihar Kano ta sanar da cewa daga yanzu ba za a sake gudanar da kowace irin muhawara daga mawakan addini a fadin jihar ba tare da samun izinin hukumar ba.
Shugaban hukumar, Alhaji Abba El-Mustapha, ya bayyana haka jim kadan bayan wata muhawara da aka gudanar tsakanin Usman Maidubun Isa da Shehi Mai Tajul’izzi ba tare da izinin hukumar ba, lamarin da ya saba da dokokin aikinta.
Don haka, hukumar ta kafa kwamitin bincike karkashin jagorancin Malam Isa Abdullahi, Daraktan Ayyuka na Musamman, tare da bai wa wadanda suka shirya muhawarar wa’adin sa’o’i 24 su bayyana gaban kwamitin domin amsa tambayoyi.
A cewar hukumar, shirya muhawarori ba tare da sahalewarta ba babban keta doka ne wanda zai iya jawo hukunci mai tsanani. El-Mustapha ya kuma jaddada aniyar hukumar wajen tabbatar da bin doka a harkar nishadi da addini a jihar.
Hukumar ta yi kira ga al’umma da su zauna lafiya, tare da bayar da hadin kai da kuma kawo bayanai masu amfani domin ci gaban al’adu, zaman lafiya da fahimtar juna a jihar Kano.
Sanarwar ta fito ne daga Ofishin Abdullahi Sani Sulaiman, Jami’in yada labarai na hukumar.