2027: Gwamnatin Tinubu Ba Ta Shirya Zaben Gaskiya Ba–Galadima

0
22

Jigo a jam’iyyar NNPP, Buba Galadima, ya zargi gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da rashin niyyar gudanar da sahihin zabe a shekarar 2027.

Yayin hira da shi a shirin Prime Time na Arise TV, Galadima ya bayyana cewa gwamnatin APC ta mamaye hukumomin gwamnati don amfani da su a siyasarta, tare da kawo cikas ga jam’iyyun adawa.

Galadima ya kuma gargadi shirin naɗa wani mutum mara inganci a matsayin shugaban INEC, yana mai cewa hakan ka iya jefa ƙasar cikin rikici.

Ya ƙara da cewa sakamakon zabukan cike gurbi a Kano da Zamfara ba gaskiya ba ne, inda ya zargi jami’an tsaro da tursasa wa masu kada kuri’a sannan daga bisani a rubuta sakamakon da ya amfanar da APC.

Dangane da ƙarfin NNPP, Galadima ya ce Rabiu Musa Kwankwaso shi ne babban jigon siyasar Najeriya da zai iya samun mafi rinjayen kuri’u idan aka gudanar da zabe cikin gaskiya da adalci.

Ya kuma musanta rade-radin cewa Kwankwaso ya gana da Shugaba Tinubu, yana mai cewa makircin siyasa ne kawai don rage masa ƙima.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here