Rahotanni daga Jihar Katsina sun tabbatar da cewa ’yan bindiga sun kai wa sojoji hari a ƙauyen Ruwan Godiya, ƙaramar hukumar Faskari, a ranar da ake gudanar da zaman sulhu tsakanin su da shugabannin al’umma.
Wani ganau ya bayyana cewa, ayarin motocin Kwamandan Rundunar Sojoji ta 382 na kan hanyar ziyartar sansanonin sojoji a yankunan Faskari, Mabai da Ɗan Ali lokacin da aka kai musu harin kwanton ɓauna.
A cewar majiyoyi, sojojin sun yi nasarar dakile harin, amma sojoji biyu sun ji rauni kuma aka garzaya da su asibitin sojoji domin jinya.
Harin ya zo ne a rana ɗaya da shugabannin Faskari suka rattaba hannu da wakilan ’yan bindiga kan yarjejeniyar zaman lafiya, wacce ta biyo bayan irin sulhun da aka kulla a wasu ƙananan hukumomi kamar Ɗanmusa, Jibia, Batsari, Ƙanƙara, Kurfi da Musawa.
Sai dai akwai shakku kan dorewar wannan sulhu, ganin cewa wasu daga cikin shugabannin ’yan bindiga sun bayyana cewa yarjejeniyar ta shafi ƙananan hukumomin da suka shiga tattaunawar kawai.
Gwamnan Katsina, Malam Dikko Umar Raɗɗa, ya ce gwamnati na ƙoƙarin samar da tsaro ta hanyar haɗin kai da al’umma, amma akwai masu ƙoƙarin kawo cikas.
Masu sharhi sun nuna cewa wannan lamari na nuna raunin tsarin sulhu da ake kullawa da ’yan bindiga, tare da buƙatar ƙarin tsaurara matakan tsaro a yankunan da ke fama da matsalar.