Masu ɗaukar amarya su 19 sun rasu sakamakon hatsarin mota a Zamfara

0
19

Akalla mutum 19 ne suka rasa rayukansu a ranar Asabar bayan wata motar ɗauke da amarya da ‘yan rakiyarta ta faɗa cikin wani kogi a ƙaramar hukumar Gummi, Jihar Zamfara.

Shaidu sun ce lamarin ya faru ne yayin da motar ke ƙoƙarin tsallake wata gada da ta karye, wadda ke tsakanin ƙauyen Gwalli da garin Gummi.

Fasinjojin sun fito daga ƙauyen Fass na ƙaramar hukumar Gummi, suna kan hanyarsu ta kai amarya Jihar Kebbi bayan kammala bikin aure.

Wani mazaunin yankin, Muhammad Fatihu, ya bayyana cewa direban motar – wanda bai saba da hanyar ba – ya shiga cikin gadar da aka yi wa cuko da yashi da duwatsu, sai dai motar ta zame ta nutse a cikin kogin.

“Direban ya tsaya ya duba, sai amarya da wasu daga cikin mutanen motar suka sauka. Amma kafin a ɗauki wani mataki, motar ta karkata ta faɗa cikin kogi,” in ji wani ɗan uwa na waɗanda abin ya shafa, Ummaru Tela Gwalli.

An ce gawawwaki 17 aka samo, yayin da guda biyu ba a gano su ba. Amarya da wasu kaɗan da suka sauka daga motar ne kaɗai suka tsira.

Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Zamfara, Hon. Adamu Aliyu Gummi, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai bayyana shi a matsayin abin takaici. Ya kuma koka kan yadda aka bar gadar cikin lalacewa tsawon fiye da shekaru biyar duk da roƙon jama’a.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here