KEDCO ya musanta zargin hannu a mutuwar marasa lafiya a asibitin AKTH saboda rashin wuta

0
13

Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Kano (KEDCO) ya musanta zargin da Asibitin Koyarwa na Aminu Kano (AKTH) ya yi cewa mutuwar wasu marasa lafiya da ke kan na’urorin taimakon numfashi ta faru ne sakamakon katse musu wutar lantarki.

A ranar Lahadi, AKTH ya bayyana cewa mutanen sun rasu ne saboda rashin wutar da aka katse, lamarin da ta ce da za a iya kauce masa da ace ba’a yanke wutar ba.

Sai dai a martaninsa, Shugaban Sashen Hulɗa da Jama’a na KEDCO, Sani Bala Sani, ya bayyana cewa wannan zargi ƙoƙari ne kawai na bata musu suna. Ya ce an dawo da wutar ma tun kafin asibitin ya fara magana.

KEDCO ta bayyana cewa matsalar ta samo asali ne daga yunƙurin da suke yi na raba layin da ke bai wa asibitin wuta daga na gidajen ma’aikatan AKTH. A cewar kamfanin, asibitin da sauran cibiyoyin lafiya suna kan layin fifikon samun wutar lantarki na 33kV da ke bada wutar kusan awa 22 a kullum.

Sai dai AKTH ya nace cewa gidajen ma’aikata su ci gaba da kasancewa a kan layi ɗaya da na asibitin, wanda hakan ke kawo matsaloli ga daidaito da sahihancin wutar da ake bai wa sashen lafiya.

KEDCO ya ƙara da cewa wannan matsala ta jawo manyan lahani da suka haddasa katsewar wutar da suka sha ƙoƙarin gujewa. Saboda haka yanzu suna ci gaba da aikin raba layin domin tabbatar da sahihin wuta mara yankewa ga asibitin.

Haka kuma, KEDCO ya yi zargin cewa ba a biyan kuɗin wutar da gidajen ma’aikatan asibitin ke amfani da ita, abin da ya ke shafar ingancin dorewar tattalin arzikin kamfanin.

Kamfanin ya bayyana cewa bashin da ake bin AKTH ya kai ₦949,880,922.45 a watan Agusta 2025, inda aka bukace ya biya cikakken kuɗin watan na ₦108,957,582.29 cikin kwanaki goma don kauce wa cire su daga jerin masu amfani da wuta.

Duk da haka, KEDCO ya jaddada cewa yana da niyyar ci gaba da ba wa AKTH wutar lantarki ba tare da yankewa ba, kasancewar babban asibiti ne na ƙasa, amma ana buƙatar kariya da kuma tsari mai dorewa wajen gudanar da ayyukan kamfanin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here