Gwamnatin tarayya ta dakatar da harajin kaso 4 cikin 100 a kayayyakin da ake shigowa da su Najeriya

0
25
Bola Tinubu
Bola Tinubu

Gwamnatin tarayya ta dakatar da sabon harajin kashi 4 cikin 100 da hukumar kwastam ta fara karɓa daga kan kayayyakin da ake shigo da su ƙasar nan.

Sanarwar da babban sakataren ma’aikatar kuɗi, R. O. Omachi, ya fitar ta bayyana cewa an ɗauki wannan mataki ne bayan tattaunawa da masana harkokin kasuwanci, masana tattalin arziki da kuma hukumomin gwamnati.

Omachi ya ce aiwatar da wannan haraji zai iya kawo cikas ga sauƙaƙe harkokin kasuwanci, ya kuma iya haifar da matsalolin tattalin arziki. A cewarsa, ‘yan kasuwa da masu shigo da kaya sun nuna damuwarsu kan wannan karin kuɗi da zai iya ƙara tashin farashi da kuma rage damar yin gasa a harkokin kasuwanci.

Ya ƙara da cewa dakatarwar za ta ba da dama a sake duba tsarin gaba ɗaya tare da haɗa kai da masu ruwa da tsaki domin samar da hanyar da za ta iya kawo kuɗaɗen shiga ba tare da cutar da tattalin arzikin ƙasa ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here