Bago: Arewa Ba Za Ta Karɓi Mulki A 2027 Ba

0
18

Gwamnan Jihar Neja, Umar Bago, ya bayyana cewa ba zai yiwu mulki ya koma Arewa a shekarar 2027 ba, domin Shugaba Bola Ahmed Tinubu yana da ikon kammala wa’adin mulki na shekaru takwas da tsarin Najeriya ya amince da shi.

Da yake magana a cikin shirin Politics on Sunday na gidan talabijin na TVC, Gwamna Bago ya ce shi ne Darakta Janar na yaƙin neman zaɓen Tinubu a 2027, inda ya bayyana cewa shalkwatar kamfen ɗin za ta kasance a Minna, babban birnin Jihar Neja.

Ya kara da cewa tsarin karɓa-karɓa na mulki tsakanin shiyyoyi ya tabbatar da daidaito a siyasar ƙasar, don haka duk wani yunƙurin neman dawo da mulki Arewa a yanzu ba zai yi nasara ba. Bago ya ce matasa a Arewa suna tare da Tinubu, kuma Jihar Neja za ta taka gagarumar rawa wajen tunkarar babban zaɓen 2027.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here