Sanata mai wakiltar Kano ta Kudu, Suleiman Abdulrahman Kawu Sumaila, ya bayyana damuwarsa kan yadda talauci ke cigaba da ta’azzara a ƙananan hukumomi duk da makudan kuɗaɗen da ake rabawa daga tarayya.
A wata hira da aka yi da shi, Kawu ya ce a cikin watanni shida na farko na shekarar 2025, ƙananan hukumomi 44 na jihar Kano, sun karɓi kusan Naira biliyan 130.74, amma hakan bai nuna tasiri a rayuwar al’umma ba saboda rashin ikon cin gashin kai.
A cewar rahoton da ya gabatar, ƙananan hukumomin Kano ta Tsakiya sun karɓi ₦49.42bn, Kano ta Kudu ₦45.46bn, yayin da Kano ta Arewa ta samu ₦35.87bn. Nassarawa LGA ce ta fi karɓa da ₦5.12bn, sai Tofa da ta samu mafi ƙanƙanta da ₦2.34bn.
Sanatan ya bayyana cewa matsalar ba ta tsaya a Kano kaɗai ba, domin daga 2023 zuwa 2025 an samu ƙaruwa da kashi 95 zuwa 125% na kuɗaɗen da ake tura wa ƙananan hukumomi a fadin ƙasar. Duk da haka, matasa fiye da kashi 40 cikin 100 na ci gaba da fama da rashin aikin yi, asibitoci sun cika, makarantun gwamnati na fama da ƙarancin kuɗi, yayin da talauci bai ragu ba.
> “Idan aka bai wa ƙananan hukumomi ikon sarrafa kuɗaɗensu kai tsaye, za su iya samar da ayyukan yi ga matasa, tallafa wa ‘yan kasuwa, gaggauta taimakawa a lokacin matsaloli, da inganta makarantu da asibitoci. Amma rashin ikon cin gashin kai ya sanya al’umma na cigaba da zama cikin ƙalubale,” in ji shi.