Tsohon Sakataren Gwamnatin Kano, Alhaji Sadauki Kura, Ya Rasu

0
8

Rahotanni sun tabbatar da cewa tsohon sakataren gwamnatin Kano, Alhaji Sadauki Kura, ya rasu da safiyar yau Lahadi a Asibitin Sojojin Sama (Airforce Hospital) da ke Kano, yana da shekaru 85 a duniya.

Alhaji Sadauki Kura ya taɓa yin aiki a matsayin manajan Union Bank, kafin daga baya a ɗauke shi zuwa ya zama sakataren gwamnatin Kano a lokacin mulkin tsohon gwamna Hamza Abdullahi.

Marigayin ya rasu ya bar mata biyu tare da ’ya’ya da jikoki masu yawa.

An riga an gudanar da jana’izarsa da misalin ƙarfe 11:00 na safe a gidansa da ke Gandu, kusa da Kwalejin Rumfa, Kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here