Mai martaba Sarkin Kano kuma tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, Muhammadu Sanusi II, ya ƙalubalanci shugabannin ƙasar, inda ya bayyana cewa Najeriya ta shafe shekaru tana fama da shugabancin da babu hangen nesa da ƙwarewa a cikin sa.
Sanusi ya bayyana haka ne a yayin bikin Kano International Poetry Festival na biyu da aka gudanar a Kano, inda ya ce, “Najeriya ta dade tana tafiya ƙarƙashin shugabanni marasa inganci. A wasu lokuta, idan ka kalli mutanen da ke shugabantar ƙasa sai ka tambayi kanka, yaya muka kai wannan hali?”
Ya kuma bayyana cewa Najeriya da ta riga ta shiga mummunan halin tattalin arziki da ta iya fuskantar faduwar gaba ɗaya, sai dai cire tallafin man fetur da gwamnatin Bola Tinubu ta yi ya taimaka wajen rage hatsarin karyewar tattalin arzikin.
Sanusi ya kara da cewa biliyoyin kuɗaɗen da aka ake kashewa a kan tallafin mai da ace an mayar da su wajen gina matatun mai, da yanzu Najeriya ba za ta kasance cikin wannan hali ba.
Ya kuma ja hankalin matasan Najeriya da su tashi tsaye wajen karɓe shugabanci daga hannun tsofaffin ‘yan siyasa masu tsohon tunani. “Har yanzu muna zaune cikin tattaunawar ƙabilanci da addini irin ta shekarun 1960, yayin da sauran ƙasashe ke tattauna makomar duniya,” in ji shi.
Hakazalika, ya gargadi gwamnati kan ci gaba da yawan aro kuɗaɗe, yana mai cewa hakan na iya jefa makomar ƙasar cikin hatsari.