Likitoci masu neman ƙwarewa sun dakatar da yajin aikin da suka fara

0
20

Kungiyar Likitoci masu neman ƙwarewa ta Najeriya (NARD) ta dakatar da yajin aikin gargadi da ta shiga, inda ta umarci mambobinta da su koma bakin aiki daga yau Lahadi.

Shugaban kungiyar, Dr. Tope Osundara, ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar da daren Asabar, inda ya ce gwamnatin tarayya ta fara amsa wasu daga cikin bukatun da suka gabatar.

> “Wasu daga cikin bukatunmu an biya su, sauran kuwa gwamnati ta yi alkawarin duba su. Mun dakatar da yajin aikin a matsayin alamar kyakkyawar niyya, domin mu sauƙaƙa wa al’ummar da ke neman lafiya a asibitocinmu,” in ji Osundara.

Rahotanni sun nuna cewa yajin aikin ya jefa harkokin kiwon lafiya a rudani a fadin ƙasa, inda manyan likitoci da sauran ma’aikatan lafiya suka dauki nauyin karɓar marasa lafiya masu tarin yawa.

Sai dai har zuwa lokacin fitar da sanarwar, ba a fayyace irin bukatun da gwamnati ta amsa ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here