Gwamnatin Tarayya ta yi gargaɗi cewa jihohi 11 za su iya fuskantar ruwan sama mai ƙarfi wanda ka iya jawo ambaliyar ruwa daga yau Lahadi zuwa Alhamis.
A cewar sanarwar da Ma’aikatar Muhalli ta fitar ta hannun Cibiyar Fadakar da Ambaliya ta Ƙasa (National Flood Early Warning Centre), jihohin da abin zai shafa sun haɗa da:
Adamawa: Ganye, Natubi
Benue: Abinsi, Agyo, Gogo, Ito, Makurdi, Udoma, Ukpiam
Nasarawa: Agima, Rukubi, Odogbo
Taraba: Beli, Serti, Donga
Delta: Umugboma, Umukwata, Abraka, Aboh, Okpo-Krika
Niger: Rijau
Kebbi: Ribah
Kano: Gwarzo, Karaye
Katsina: Jibia
Sokoto: Makira
Zamfara: Kaura Namoda, Shinkafi, Maradun, Gusau, Anka, Bungudu
An ba da shawarar cewa al’ummar da ke kusa da koguna su gaggauta barin wuraren don guje wa hadurra.
Haka kuma, an bukaci gwamnatocin jihohi da hukumomi masu ruwa da tsaki su ɗauki matakan gaggawa don rage illar da hakan zai iya haifarwa.