Rahoto ya nuna cewa tun daga 1999 zuwa 2023, Najeriya ta kashe Naira biliyan 981.5 wajen gudanar da zabuka bakwai. Duk da wannan tsadar kudi, ingancin zabukan ya ragu tare da yawaitar koke-koke a kotu.
Yadda kashe kuɗin ke ƙaruwa:
- 1999 – Naira biliyan 32 – Koke 2
- 2003 – Naira biliyan 55.2 – Koke 560
- 2007 – Naira biliyan 74.2 – Koke 1,290
- 2011 – Naira biliyan 99.7 – Koke 732
- 2015 – Naira biliyan 122.9 – Koke 560
- 2019 – Naira biliyan 242.2 – Koke 1,697
- 2023 – Naira biliyan 355.3 – Koke 1,996
Jimilla: Naira biliyan 981.5, tare da koke 6,840 a kotu.
Hasashen gaba
INEC ta nemi Naira biliyan 126 domin shirye-shiryen zaben 2027, amma majalisa ta amince da Naira biliyan 140. Masana sun ce zaben 2027 na iya cinye har Naira biliyan 700.
Matsalolin tsadar zabuka
- Cin hanci da lalata kayan zabe.
- Matsalar sufuri da yanayin kasa.
- Sabuwar rajistar masu kada kuri’a a duk shekara.
- Kai hare-hare kan ofisoshin INEC da kona kayan aiki.
Kwatantawa da wasu ƙasashe
- Pakistan (2024): $164bn
- Rasha (2024): $336bn
- Kanada (2021): $498bn
- Bangladesh (2024): $21bn
- Kenya (2022): $257bn
- Ghana (2024): $52bn
- Afrika ta Kudu (2024): $138bn
Najeriya ta kashe fiye da kuɗin wadannan kasashe, duk da cewa ba ta da yawan masu kada kuri’a kamar India ko Amurka.