Jigawa: Gwamnati ta kashe kusan Naira biliyan 2 a tafiye-tafiye da alawus a watanni 6 

0
16

Wani rahoton da aka fitar ya nuna cewa gwamnatin jihar Jigawa ta kashe makudan kuɗaɗe kan alawus, karramawa da kuma tafiye-tafiyen ƙasashen waje a cikin watanni shida kacal, fiye da kuɗin da ta ware wa hukumomin samar da ruwa da ke fama da matsalar samar da ruwan sha mai tsafta a yankunan karkara.

Binciken da jaridar SolaceBase ta yi ya nuna cewa gwamnati ta ware Naira miliyan 846.7 domin tafiye-tafiyen ƙasashen waje, yayin da aka kashe Naira biliyan 1.097 wajen alawus da karramawa. Jimillar adadin ya kai Naira biliyan 1.94 a cikin rabin shekara.

Masu sharhi sun nuna damuwa da irin wannan salo na kashe kuɗi, musamman ganin yadda jihar ke fuskantar matsalolin talauci, yawan kamuwa da cututtuka da kuma ƙarancin ilimi. A cewar su, idan aka mayar da hankali kan harkokin samar da tsaftar ruwa da kiwon lafiya, zai fi amfani ga al’ummar jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here