Gini mai hawa uku ya rushe tare da danne mutane a Legos

0
18

Wani gini mai hawa uku da ake aikin gina wa shi ya rufta a unguwar Yaba, jihar Legas, da misalin ƙarfe 8:00 na daren jiya, lamarin da ya jefa al’ummar yankin cikin tashin hankali.

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta ƙasa (NEMA) ta tabbatar da cewa aƙalla mutum biyar ne aka ruwaito suna cikin ginin lokacin da ya rufta, sai dai wasu shaidun gani da ido sun ce adadin na iya kaiwa shida.

Rahotanni sun tabbatar da cewa hukumar ta ceto mutum huɗu daga cikin waɗanda abin ya rutsa da su, kuma an garzaya da su asibiti domin kulawar likitoci.

Sai dai har yanzu babu tabbas kan yawan mutanen da suka rage a ƙarƙashin ɓaraguzan ginin, yayin da jami’an ceto ke ci gaba da aikin bincike da ƙoƙarin samun sauran.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here