An Samu Gawar Ɗalibar Jami’ar Taraba A Ɗakin Saurayin ta

0
21

Wani lamari mai tayar da hankali ya auku a Jalingo, jihar Taraba, inda aka tsinci gawar wata ɗaliba ta Jami’ar Taraba (TSU) a ɗakin saurayinta.

Ɗalibar mai suna Comfort Jimtop, ’yar ƙaramar hukumar Takum, na karatun fannin aikin jarida a jami’ar. Rahotanni sun ce an gano gawarta ne da rana, inda aka samu kwalaben giya a kusa da gadon da take kwance.

Gidan da lamarin ya faru na da mazauna kusan 15 ciki har da saurayinta, Emmanuel Shata. Sai dai bayan gano gawar, dukkanin mazauna gidan sun tsere.

Kakakin rundunar ’yansandan jihar, ASP Leshen James, ya tabbatar da faruwar al’amarin, yana mai cewa suna gudanar da bincike tare da neman saurayin da sauran mazauna gidan da suka gudu.

“Lokacin da jami’anmu suka isa wajen, babu kowa a cikin gidan. Saurayin da sauran mazauna gidan sun riga sun tsere,” in ji shi.

Lamarin ya jefa ɗalibai da mazauna yankin cikin tashin hankali da firgici, yayin da hukumomi ke ci gaba da bincike kan hakikanin abin da ya faru.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here