A karon farko an samu mace mai horar da ƴan kwallon kafa a Kano

0
20

Kocin kwallon ƙafa mace ta farko a jihar Kano, Hyda Ahmad, ta bayyana shirin kafa ƙungiyar kwallon ƙafa ta mata zalla domin ƙarfafa wa mata gwuiwa wajen shiga harkar wasanni da kuma zaburar da ƙananan ’yan mata su cika burinsu cikin kwallo ba tare da tsoro ko takurawa ba.

Hyda Ahmad, wadda ta kafa makarantar koyon kwallo duk da ƙalubale da dama, ta ce wannan mataki zai zama babbar dama ga ’yan kwallo mata su nuna baiwarsu, su shiga manyan gasa, tare da samun damar yin fice a duniya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here